Connect with us

News

Jirgin Dakarun Sojin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa A Gonaki A Benue

Published

on

1791452576880

Rundunar sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta ce wani jirginta mai saukar ungulu ya yi saukar kariya (precautionary landing) a wata gona a jihar Benue, bayan kammala wani samame na tallafa wa dakarun kasa wajen yakar masu garkuwa da mutane.

Shaidun gani da ido sun ce jirgin ya sauka a wata gona da ke yankin Utur Tse-Igboji, a Makurdi, babban birnin jihar.

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Wani Mutum Kan Zargin Kona Gidan Yayansa A Jigawa 

Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Ehimen Ejodame, ya bayyana a cikin wata sanarwa ranar Laraba cewa an gudanar da aikin ne a kan wasu da ake zargi da yin garkuwa da mutane a karamar hukumar Ogbadigbo, kusa da iyakar Benue da Enugu.

A cewar rundunar, aikin ya kawo cikas ga ayyukan masu laifin tare da taimaka wa dakarun kasa wajen ci gaba da kutsawa yankin.

Ejodame ya ce bayan kammala aikin, matukin jirgin ya yi amfani da kwarewarsa wajen yin saukar kariya mai nisan kusan mil 10 daga filin saukar jirgin, bisa ka’idojin tsaro da ake bi bayan gudanar da ayyukan yaki.

Advertisement

Ya kara da cewa jirgin ya koma sansaninsa lafiya.

Lamarin ya faru ne kwanaki biyu kacal bayan hatsarin wani jirgin NAF a Igbokoda, karamar hukumar Ilaje ta jihar Ondo, inda mutane 25 da ma’aikatan jirgin bakwai ke cikinsa.

 

 

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending