News
NLC Ta Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Yi Watsi Da Manufofin Da Ke Ƙara Tsadar Man Fetur
Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da manufofin da take ganin suna haddasa hauhawar farashin man fetur a ƙasar.
Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, ya ce gwamnati ba za ta ci gaba da neman ma’aikata su yi sadaukarwa ba tare da ɗaukar matakan rage musu raɗaɗin matsin tattalin arziƙi ba.
Dakarun Soji Sun Dakile Harin Lakurawa A Kebbi, Sun Kwato Babura 17
A cewarsa, hauhawar farashin man fetur na ƙara tsadar sufuri, abinci da sauran muhimman kayayyakin masarufi, lamarin da ke ƙara jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali.
NLC ta buƙaci gwamnatin ta yi aiki tare da hukumomin da abin ya shafa domin samar da matakan da za su rage farashin man fetur da kuma sauƙaƙa wa al’umma halin da suke ciki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin sayar da man fetur a farashi mai rahusa a gidajen man kamfanin NNPC na tsawon kwanaki 30.
Haka kuma, gwamnatin na tattaunawa kan sanya iyakar farashin saukar da man fetur zuwa naira 1,350 kan kowace lita, inda za a riƙa duba farashin a kowane wata.
Sai dai ƙungiyar kwadagon ta jaddada buƙatar samar da matakan da za su rage wa ma’aikata da sauran ’yan Najeriya nauyin tsadar rayuwa.
