Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Dakile Harin Lakurawa A Kebbi, Sun Kwato Babura 17

Published

on

MixCollage 08 Oct 2026 07 11 PM 3182

Dakarun Soji sun dakile harin da wasu da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne suka kai kan sansanin soji da ke Maiyama, a Jihar Kebbi, inda suka ƙwato babura 17 da makamai daban-daban.

Harin ya faru ne da safiyar Laraba, 7 ga Oktoba, 2026, lokacin da maharan suka isa sansanin da ke kan babura sama da 100, suka buɗe wuta kan sojojin.

Marasa Hankali Ne Kadai Zasu Zabi Shugaba Tinubu A Zaben 2027  — Rotimi Amaechi

Sanarwar da rundunar Operation FANSAN YAMMA ta fitar ta ce maharan sun yi amfani da makamai daban-daban, ciki har da manyan bindigogi da makaman harba rokoki.

Sai dai sojojin da ke ƙarƙashin Sashe na Biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma sun mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa maharan ja da baya ba tare da cimma manufarsu ba.

A cewar sanarwar, maharan sun tsere ne suka bar wasu makamai da kayayyakin aikinsu, yayin da sojojin suka bi sahunsu tare da gudanar da bincike a yankin.

Advertisement

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da babura 17, bindigar PKT, bindiga ƙirar AK-47, harsasai iri-iri da wata na’urar sadarwa da ake zargin maharan sun yi amfani da ita wajen kai harin.

Rundunar ta bayyana cewa ƙwato kayayyakin na iya rage ƙarfin maharan na gudanar da ayyukansu a yankin.

Ta ƙara da cewa sojoji na ci gaba da sintiri da ayyukan kakkabe ’yan ta’adda, tare da ƙoƙarin gano waɗanda suka tsere bayan harin.

Operation FANSAN YAMMA ta jaddada aniyarta ta ci gaba da kare al’ummomi da hana ’yan ta’adda samun ’yancin zirga-zirga a yankunan da ke ƙarƙashin kulawarta.

 

 

Advertisement

 

CHANNELSTV

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending