Connect with us

News

Marasa Hankali Ne Kadai Zasu Zabi Shugaba Tinubu A Zaben 2027  — Rotimi Amaechi

Published

on

Rotimi Amaechi 2026 10 08 372 e1791494571950

Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar ADC Rotimi Amaechi, ya ce “mahaukaci ne kaɗai” zai sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Amaechi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron tattaunawa da jama’a na jam’iyyar ADC a Jihar Edo.

Saƙon “Renewed Hope” Ya Isa Ga Jama’a — Waiya Ya Bukaci Mukarraban Shugaba Tinubu Daga Arewa Su Kai Saƙon Gwamnati Ga Jama’a

Tsohon ministan sufuri ya zargi gwamnatin Tinubu da aiwatar da manufofin tattalin arziki da ya ce sun jefa ’yan Najeriya cikin ƙarin matsin rayuwa.

Ya kuma soki matakin cire tallafin man fetur, yana mai cewa matakin ba jarumtaka ba ne kamar yadda gwamnatin ta bayyana, sai dai abin da ya kira “rashin taka-tsantsan”.

“Na karanta a kafafen sada zumunta cewa a shekarar 2027 ne za mu san adadin mahaukatan da ke Najeriya. Mahaukaci ne kaɗai zai iya zaɓar Tinubu.

Advertisement

“Idan ba ka haukace ba, to Tinubu bai kamata ya ci zaɓe a nan ba,” in ji Amaechi.

Ya ce cire tallafin man fetur ya ƙara tsadar rayuwa, yana mai cewa ’yan Najeriya da dama na fuskantar matsalar samun abinci da sauran abubuwan buƙata na yau da kullum.

Amaechi ya kuma soki yadda Najeriya ke amfani da albarkatun man fetur da iskar gas da take da su, musamman a yankin Kudu maso Kudu.

A baya, Amaechi ya ce zai iya mara wa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027 idan farashin litar man fetur ya koma naira 600.

 

 

Advertisement

THE CABLE 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending