News
Jami’an Ghana Da Na FBI Sun Kama Mutum 130 Kan Zargin Alaka Da Zambar Sama Da Naira Biliyan 13
Hukumomin Ghana da Amurka sun kama mutane 130 da ake zargi da hannu a zambar intanet da ta shafi mutane 89, inda aka yi zargin an tafka asarar sama da dala miliyan 10, kwatankwacin kusan naira biliyan 14.
Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis, bayan wani samame na haɗin gwiwa da jami’an tsaron Ghana suka gudanar.
Jami’an Ghana Da Na FBI Sun Kama Mutum 130 Kan Zargin Alaka Da Zambar Sama Da Naira Biliyan 13
Daraktan FBI, Kash Patel, ya ce samamen ya kai ga kama mutane 130, ciki har da wasu mutanen da ake zargin an yi safarar su zuwa wasu wurare tare da tilasta musu shiga ayyukan zamba ta intanet.
Ya bayyana cewa samamen wani ɓangare ne na ƙoƙarin hukumar na murƙushe ƙungiyoyin masu damfara ta intanet, waɗanda ke gudanar da ayyukansu daga manyan gine-gine ko rukunin gidaje, suna zambartar mutane a sassa daban-daban na duniya.
Sai dai hukumomin ba su bayyana ƙasashen da waɗanda aka zambatar suka fito ba, ko kuma asalin ƙasashen mutanen da aka kama.
Yaƙi da masu zambar intanet
Patel ya ce wannan samame na daga cikin wani shirin FBI mai suna Operation Level Up, wanda aka ƙaddamar domin dakile zambar intanet da kuma kare waɗanda ke cikin haɗarin faɗawa tarkon masu damfara.
Ya bayyana cewa irin waɗannan laifuka na cutar da Amurkawa tare da jefa rayuwarsu cikin mawuyacin hali.
A cewarsa, shirin ya taimaka wajen ƙwato kuɗi da suka kai dala biliyan 17 a duniya, tare da yi wa sama da Amurkawa 10,000 gargaɗin cewa suna cikin haɗarin faɗawa tarkon masu zamba.
A watan Fabrairu, rundunar ‘yan sandan ƙasa da ƙasa, Interpol, ta sanar da cewa jami’an tsaro a ƙasashen Afirka 16 sun kama mutane 651 a wani samame na tsawon makonni takwas.
Samamen ya mayar da hankali kan zambar saka hannun jari, damfara ta wayar salula da kuma aikace-aikacen bayar da lamuni na bogi.
Interpol ta bayyana cewa mafi yawan waɗanda abin ya shafa a wannan samame ‘yan Afirka ne.
Lamarin ya ƙara nuna yadda zambar intanet ke zama babbar matsala a nahiyar Afirka da sauran sassan duniya.
