Connect with us

Kasuwanci

Sabunta Kasuwar Tarauni: ’Yan Kasuwa Sun Nuna Shakku Kan Rabon Shaguna

Published

on

IMG 20261122 WA0018
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Tarauni da ke Kano, Abdullahi Muhammad, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta shiga cikin lamarin sake fasalin kasuwar, musamman wajen sanya ido kan kwamitin da aka kafa domin tantance ’yan kasuwa da raba shaguna.

Ya ce ’yan kasuwar na da fargabar cewa kwamitin zai iya yi musu rashin adalci, saboda haka suke buƙatar gwamnati ta tabbatar an gudanar da aikin cikin gaskiya da adalci.

KANO PENSION APP: OGP Ta Kara Tabbata A Kano   —Yayin da OGP ke kara karfafa alaka da ‘yan jarida 

Abdullahi Muhammad ya bayyana cewa ’yan kasuwar suna maraba da shirin sabunta kasuwar, kuma suna shirye su ba da haɗin kai wajen ganin an gudanar da aikin yadda ya kamata, sai dai sun nuna rashin gamsuwa da yadda aka tsara rabon shagunan.

Ya ƙaryata zargin cewa wasu ’yan kasuwa za su rasa shaguna ko wuraren sana’arsu, yana mai cewa har yanzu babu wani tabbataccen bayani da ke nuna cewa za a kwace wa wani shago ko wurin kasuwancinsa.

Ya kuma yi zargin cewa wasu mutane na ƙara tayar da hankalin ’yan kasuwar kan lamarin, duk da cewa babu wani hukunci na ƙarshe da aka bayyana kan rabon shaguna.

Advertisement

Shugaban ƙungiyar ya ce tun bayan fara shirin sake fasalin kasuwar da kuma gabatar da ɗan kwangila da ƙaramar hukumar ta yi, wasu ’yan kasuwa suka fara nuna shakku kan yadda za a gudanar da aikin.

Ya bayyana cewa wannan ne ya sa suka miƙa lamarin ga Allah, domin Ya zaɓa musu abin da ya fi alheri, tare da gudanar da addu’o’i na neman samun zaman lafiya, bunƙasar kasuwanci da yalwar arziki a tsakanin ’yan kasuwar.

An gudanar da addu’ar Al-Qunut da sauran addu’o’i ne domin neman Allah Ya kawo mafita kan matsalolin da suka shafi rabon shaguna da sake fasalin kasuwar Tarauni, wadda ta shahara wajen harkokin kasuwanci a Kano..

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending