Connect with us

Labarai

Mutane 64 Sun Mutu A Harin Ramuwa Bayan Kisan Wani Dagaci A Neja

Published

on

One of the burnt houses (1)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Akalla mutane 64 ne aka kashe a hare-haren ramuwar gayya da aka kai kan wasu rugagen Fulani a ƙaramar hukumar Borgu ta Jihar Neja, bayan kisan wani dagaci da wasu ’yanbindiga suka yi.

Hare-haren sun faru ne tsakanin ranar Asabar da Lahadi a yankunan Wawa da Gada-Oli, bayan wani hari da aka kai ƙauyen Lumman-Ba’are, inda aka kashe dagacin garin, Malam Bawa Muhammad, da matarsa, ’ya’yansa uku da wani ɗan banga mai suna Angulu, da wasu mazauna ƙauyen.

Kwankwaso Ne Ya Sa Na Rantse Da Alƙur’ani Za Mu Koma Jam’iyyar APC —Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Rahotanni sun ce maharan sun kuma ƙona gidaje tare da yin garkuwa da wasu mutane.

Bayan kisan dagacin, wasu da ake zargin ’yan sa-kai da ’yan bangar ƙabilar Kambari ne suka kai hare-haren ramuwar gayya kan rugagen Fulani a Wawa da Gada-Oli.

 

Advertisement

Harin Gada-Oli ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na rana, a lokacin da wasu mazauna yankin ke gudanar da sallar Azahar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban ƙungiyar Miyetti Allah reshen Neja, Ardo Umar Lapai, yana cewa an kashe Fulani 64 a hare-haren, kuma tuni aka yi jana’izar waɗanda suka mutu.

Rikicin ya tilasta wa wasu mazauna yankin tserewa zuwa ƙaramar hukumar Agwara da Jihar Kebbi domin neman mafaka.

Kakakin rundunar ’yansandan Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da harin da aka kai Lumman-Ba’are, inda ya ce an tura jami’an tsaro na haɗin gwiwa domin kamo waɗanda suka aikata laifin.

Ƙungiyar Miyetti Allah ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Neja da su gaggauta ɗaukar matakan kawo ƙarshen rikicin da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending