Connect with us

Labarai

KANO: An tsinci ‘Yan Tagwayen Jarirai Sabuwar Haihuwa A Yankin Dorayi Unguwar Bello

Published

on

Jaririya
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Mazauna layin Gidan Takwas da yankin Ɗorayi unguwar Bello a ƙaramar hukumar Gwale, sun wayi gari da ganin wasu ƴan tagwayen jarirai sabuwar haihuwa da aka ajiye su aka tafi aka bar su.

Wata daga cikin mazauna yankin da ta nemi a sakaye sunan ta ce ta shaidawa Dala FM Kano, faruwar lamarin a ranar Lahadi 22 ga watan Nuwamba, 2026.

Mutane 64 Sun Mutu A Harin Ramuwa Bayan Kisan Wani Dagaci A Neja

Ta ce an ajiye ƴan tagwayen jariran ne da misalin ƙarfe 11:00 na daren ranar Asabar 21 ga watan Nuwamba, 2026.

Sai dai ta ce har zuwa wayewar ranar Lahadi, ba a iya gano waɗanda suka ajiye jariran biyu ba.

A cewar matar, lokacin da suka tsinci ƴan biyun babu kaya a jikin su, daga bisani ne al’umma suka taimaka aka samo kaya inda aka sanya musu, kuma aka kai su gidan mai unguwa mafi kusa.

Advertisement

Ta ce sun matuƙar shiga cikin tashin hankali hankali kan yadda suka tsinci ƴan tagwayen, kasancewar ba su taɓa cin karo da irin wannan lamari ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending