Connect with us

News

Kwastam Sun Kama Dala 193,000 Da Aka Ɓoye Cikin Kwalayen Yoghurt

Published

on

Kwastam Sun Kama Dala 193,000 da Aka ɓoye Cikin Kwalayen Yoghurt a Abuja

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta yi nasarar ƙwace Dala 193,000 da aka ɓoye a cikin kwalayen yoghurt a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

A cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar, jami’anta sun gano kuɗin ne a ranar Alhamis bayan samun bayanan sirri da kuma gudanar da bincike kan wani kaya da ake zargi.

Advertisement

Ruwan Da Karnuka Su Ke Wanka A Ciki Shi Mutanen Ke Sha A Ƙaramar Hukumar Warawa A Kano

Wanda ake zargi, Kamilu Abdullahi Sarina, mai shekaru 40, ya iso Najeriya ne ta jirgin ƙasar Habasha bayan tashinsa daga Jidda, Saudiyya.

“Da safiyar ranar mun samu sahihan bayanai game da shigowar kuɗin. Da yamma, yayin da ake caje jakunkuna, muka gano wani nauyi da bai dace da irin wannan kaya ba. Bayan sake bincike, mun bankaɗo kuɗin da aka ɓoye cikin kwalayen yoghurt,” in ji Olumide Adebisi, jami’in da ke kula da rundunar Abuja.

Advertisement

A cewar Adebisi, wannan ya saɓa wa dokokin kwastam na shekarar 2023 da dokar hana safarar haramtattun kuɗi ta 2022, wacce ta tilasta kowane matafiyi da ke ɗauke da fiye da Dala 10,000 ya bayyana hakan ga hukumomi.

“Idan mutum ya gaza sanarwa, za a iya ƙwace kuɗin ko kuma a yanke masa hukuncin dauri na shekaru biyu ko duka biyun,” in ji Adebisi.

Advertisement

Yanzu haka, hukumar ta mika kuɗin ga EFCC don gudanar da bincike, tare da gargaɗin matafiya da su bi doka wajen shigowa da kuɗi ƙasar.

Kwanturola-Janar na Kwastam, Bashir Adeniyi, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da binciken, tare da jaddada kudirin hukumar na dakile safarar kuɗi da sauran haramtattun kayayyaki.

Advertisement

 

 

Advertisement

PREMIUM TIMES 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending