Connect with us

News

Abubuwa 12 da ya kamata ku sani game da sabuwar Dokar Zaɓe da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu (Electoral Law 2026)

Published

on

Shugaba Tinubu ya bayyana makomar TETFUND da NITDA da NASENI

Abubuwa 12 da ya kamata ku sani game da sabuwar Dokar Zaɓe da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu (Electoral Law 2026)

1️⃣ Kudin Zaɓe Tun da Wuri

Advertisement

Za a saki dukkan kuɗaɗen zaɓe ga INEC akalla watanni 6 kafin ranar zaɓe ta farko.

2️⃣ Shirye-shiryen Jam’iyyu

Advertisement

Jam’iyyun siyasa dole su miƙa jerin ’yan takararsu na ƙarshe kwanaki 120 kafin zaɓe.

3️⃣ Tabbatar da Gaskiya (Transparency)

Advertisement

INEC za su wallafa jerin sunayen sahihan ’yan takara kwanaki 60 kafin zaɓe.

4️⃣ Sauƙaƙa samun katin zaɓe (PVC)

Advertisement

Masu jefa ƙuri’a za su iya sauke (downloading) katin zaɓen su (PVC) kai tsaye daga shafin INEC.

5️⃣ Kawo ƙarshen tsaikon kaɗa ƙuri’a

Advertisement

Matsalar na’ura ko rasa kati ba za su hana ka kaɗa ƙuri’a ba muddin sunanka yana rijista.

6️⃣ Haɗa NIN da Rijistar Zaɓe

Advertisement

An haɗa NIN da rijistar masu zaɓe don hana rijista sau biyu da maguɗi.

7️⃣ Kawo Ƙarshen “Indirect Primaries”

Advertisement

An soke zaɓen wakilai (delegates) da ke zaɓen fidda gwani, za a koma “direct primaries” wato zaɓen ƙato bayan ƙato, ko “consensus” a matsayin hanyar da aka amince da su.

8️⃣ Ƙara Ƙarfi ga Mambobin Jam’iyya

Advertisement

A direct primaries, kowane memba yana da ƙuri’a, haka zalika consensus ba zai tabbata ba sai da yarda a rubuce ta duk masu neman takara.

9️⃣ Iyakance lokacin Gudanar da Shari’o’in Zaɓe

Advertisement

Dukkan ƙorafe-ƙorafen zaɓe (kafin da bayan zaɓe) dole a kammala su kafin 29 Mayu, 2027.

🔟 Hukunci mai tsauri kan Saye/Sayar da PVC

Advertisement

Tara ta tashi daga ₦2m zuwa ₦5m ga duk wanda aka samu da laifi.

1️⃣1️⃣ Rijista Sau Biyu

Advertisement

Tsarin NIN zai gano, ya soke, kuma ya kai ga hukunta duk mai rijista fiye da sau ɗaya.

1️⃣2️⃣ Ɗora sakamakon zaɓe a BVAS

Advertisement

Wajibi a ɗora sakamakon zaɓe a na’urar latroni ta BVAS, in an samu tangarɗar sadarwa, sai a yi amfani da takardar EC8 a madadi.

Wannan doka na nufin tabbatar da gaskiya, sauƙi ga masu zaɓe, da kuma samar da tsauraran matakai dan hana maguɗi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending