Connect with us

News

Ƴarinya ‘Yar Shekara 17 Ta Yi Garkuwa Da Kanta Tare Karɓar Kuɗin Fansa Daga Hannun Mahaifiyarta ‎ ‎

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta dake kudancin Najeriya ta kama wata yarinya mai shekara 17 da ake zargi da shirya garkuwa da kanta tare da wasu abokanta uku, domin karɓar kuɗin fansa daga mahaifiyarta.

‎Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Bright Edafe ne, ya bayyana cewa yarinyar – dalibar aji uku a makarantar sakandare (SSS 3) – ta amsa cewa ita da abokanta ne suka tsara lamarin domin su samu kuɗi ta hanyar damfarar mahaifiyarta

Advertisement

Abubuwa 12 da ya kamata ku sani game da sabuwar Dokar Zaɓe da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu (Electoral Law 2026)

‎A cewar ‘yan sanda, yarinyar da abokanta sun yi tafiya zuwa birnin Port Harcourt inda suka sauka a wani otel. Daga nan ne ta kira mahaifiyarta tana iƙirarin cewa wasu sun yi garkuwa da ita, tare da neman a biya kuɗin fansa domin sakinta.

Advertisement

‎Rahotanni sun ce mahaifiyar yarinyar – wadda gwauruwa ce mai ƙaramin hali – ta yi ƙoƙarin tara kuɗin domin biyan fansar, kafin daga bisani ta kai ƙara ga jami’an tsaro.

‎Binciken da aka gudanar ya nuna cewa ba garkuwar ba ta gaskiya ba ce, sai dai shirin damfara da aka tsara domin karɓar kuɗi.

Advertisement

‎‘Yan sanda sun ce yarinyar ta amsa cewa sun kashe kuɗin da suka samu wajen sayen tufafi da wasu kayayyaki.

‎Rundunar ta bayyana damuwa kan yadda irin waɗannan laifuffuka ke ƙara yawaita tsakanin matasa, inda wasu ke kwaikwayon dabarun damfara domin karɓar kuɗi daga iyayensu.

Advertisement

 

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending