Entertainment
Jarumin Nollywood ya soki Seyi Tinubu kan mayar da hankali ga sake zaɓen mahaifinsa duk da halin ƙunci da ƴan Nijeriya ke ciki
Jarumin masana’antar fina-finan Nollywood, Austine Emmanuel, ya bayyana damuwarsa kan matsin tattalin arziki da ake ciki a Najeriya, inda ya yi kakkausar suka ga Seyi Tinubu, ɗan Shugaban ƙasa Kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Emmanuel ya buƙaci Seyi Tinubu da ya fi mai da hankali kan abin da tarihin mahaifinsa zai bari a baya, maimakon mayar da hankali kan batun sake tsayawa takara.
Dakarun Soji Sun Ceto Wata Mata Tare Da Kama Waɗanda Su Ka Yi Garkuwa
Jarumin ya fara ne da sukar abin da ya kira goyon bayan da ba na gaskiya ba da ke kewaye da Seyi, yana mai cewa mutane da dama suna nuna masa soyayya ne saboda abin duniya, ba don gaskiya ba.
Ya ce, “Abin da kake damuwa da shi kawai shi ne yadda mahaifinka zai sake zama shugaban ƙasa, amma ba ka damu da irin tarihin da zai bari ba. Mutanen da ke kewaye da kai ba za su gaya maka gaskiya ba saboda abin da suke nema shi ne kuɗinka.”
Emmanuel ya ƙara da cewa, yawancin masu goyon bayan shugaban ƙasar ba don sun yarda da jagorancinsa ba ne suke goyon bayansa, sai dai saboda anfani na kuɗi.
A cewarsa, “Idan shugaban ƙasa ya yi aiki mai kyau, ba sai ka rika kashe kuɗi don mutane su goyi bayanka ba.”
