Politics
APC Convention: Gwamnoni 32 da wakilai sama da 8,000 sun mamaye Abuja, inda aka tsananta domin babban taron jam’iyya mai mulki
Birnin tarayya Abuja ya cika makil yayin da shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni 32, da wakilai sama da 8,400 suka hallara domin babban taron jam’iyyar APC na ƙasa na shekarar 2026.
Ana gudanar da taron a Eagle Square, inda ake sa ran zai tsara makomar shugabancin jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.
Ta’ammali Da Muggan Kwayoyi Na Daga Cikin Matsalolin Dake Ci Gaba Da Yada Cutar Kanjamau – NDLEA
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa wakilai 8,453 ne aka tantance, yana mai cewa taron wata muhimmiyar dama ce ta ƙarfafa haɗin kai da manufofin gwamnatin shugaba Tinubu na “Renewed Hope”.
Saboda tsaro da shirye-shirye, gwamnatin tarayya ta umarci ma’aikatan gwamnati da ke Abuja su yi aiki daga gida, tare da rufe wasu manyan hanyoyi a kusa da sakatariyar gwamnati.
Otal-otal a birnin sun cika, yayin da dubban magoya baya da wakilai ke ci-gaba da shigowa.
Ana sa ran taron zai fitar da sabbin shugabanni tare da tsara alkiblar siyasa kafin zaɓen 2027.
