Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Sabbin Lasisin shigo Da Mai Guda 6 Domin Rage Tsadar Man Fetur

Published

on

Tinubu Bola 750x430
Advertisements
Advertisements
Spread the love

Hukumar da ke kula da harkokin sufuri da kasuwancin man fetur ta sanar da bayar da sabbin lasisin shigo da man fetur guda shida, a wani mataki da ake ganin zai taimaka wajen rage tsadar mai da kuma magance ƙarancinsa da ake fama da shi a wasu sassan ƙasar.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar tangarɗa wajen samar da isasshen man fetur, lamarin da ake dangantawa da rikice-rikicen da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ke ci gaba da shafar farashin mai a kasuwannin duniya.

Ƙungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki

Advertisement

Haka kuma, matakin ya biyo bayan yadda matatar mai ta attajirin Afirka, Aliko Ɗangote, ke fitar da wani kaso na man da take tacewa zuwa ƙasashen waje, duk da bukatar da ake da ita a cikin gida.

Duk da kasancewar Najeriya cikin ƙasashen da suka fi arzikin man fetur, har yanzu al’ummarta na fuskantar matsalolin tsadar mai da ƙarancinsa. Wannan na zuwa ne duk da kasancewar babbar matatar mai ta Ɗangote wadda ake sa ran za ta taimaka wajen wadatar da kasuwar cikin gida.

Shugaban ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa, Alhaji Abubakar Mai Gandi, ya bayyana cewa suna maraba da wannan mataki, yana mai cewa zai iya taimaka wa wajen ƙara wadatar mai a kasuwa.

Advertisement

Sai dai ya yi gargaɗin cewa wajibi ne a tabbatar da ingantaccen tsarin kulawa da sa ido, domin ganin cewa sauƙin farashin mai ya kai ga masu amfani da shi kai tsaye.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending