News
Mahaifiyar tsohon gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai ta rasu.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya fada cikin jimami bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai, wadda ta rasu a ranar Juma’a, 27 ga watan Maris, 2026.
Sanarwar rasuwar ta fito ne ta hannun ɗansa, Bello El-Rufai, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya tabbatar da faruwar lamarin.
Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Sabbin Lasisin shigo Da Mai Guda 6 Domin Rage Tsadar Man Fetur
Rahotanni daga majiyoyin iyali sun nuna cewa marigayiyar ta jima tana fama da larurar da ke da alaƙa da tsufa, kafin rasuwarta a ranar Juma’a.
Wasu majiyoyi sun kuma bayyana cewa lafiyarta ta ƙara tabarbarewa a ‘yan kwanakin nan, musamman bayan samun labarin tsare ɗanta da Independent Corrupt Practices Commission (ICPC), ko da yake babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da alaƙar hakan da rasuwar.
Iyalan sun bayyana alhini kan wannan rashi, tare da roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta mata, Ya kuma ba ta Aljannatul Firdausi.
