Connect with us

Politics

Matasa Sun Bukaci Ibrahim Little Ya Tsaya Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC

Published

on

IMG 1545 768x1024 (1)
Advertisements
Advertisements
Spread the love

Ƙungiyar Kano Youth Concern Initiative sun buƙaci jigo a jam’iyyar ADC, Ibrahim Ali Amin (Little), da ya fito takarar gwamnan Jihar Kano a zaɓe mai zuwa.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugabanta, Abubakar Junaid Binoni, ya sanya wa hannu tare da sakatarenta, Saidu Muhammad Ahmad, a ranar Alhamis.

“Azumin Sitta Shawwal: Fa’idodi, Sharudda, Da Muhimmancinsa A Musulunci”

Advertisement

A cewar sanarwar, matasan sun ce lokaci ya yi da Little zai shiga takarar gwamna domin “ceto Kano daga tasirin ‘yan siyasar da suka daɗe suna riƙe da madafun iko,” waɗanda suka zargi da dakile ci gaban jihar.

“Muna buƙatar shugaba mai zaman kansa, mai hangen nesa da jajircewa, wanda zai iya jagorantar bunƙasar tattalin arzikin Kano cikin sauri,” in ji Binoni.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa ƙwarewar Little a ɓangaren kasuwanci mai zaman kansa na daga cikin dalilan da suka sa suke ganin ya dace da kujerar gwamna, suna mai cewa hakan zai ba shi damar fahimtar yadda za a samar da ayyukan yi da jawo jari.

Advertisement

Sun ƙara da cewa yawancin tsoffin gwamnonin jihar sun fito ne daga aikin gwamnati ko kuma tsarin siyasar godfatherism, wanda suka ce ya takaita cigaban jihar a wasu lokuta.

A cewarsu, Little na da ƙwarewar shugabanci, dabarun tafiyar da al’amura da kuma fahimtar yadda za a bunƙasa tattalin arziki ta hanyar sabbin hanyoyi, ciki har da ƙarfafa masana’antu da kasuwanci.

Ƙungiyar ta kuma yi nuni da cewa dogon burinsa na shugabantar Kano, wanda ya ɗauki fiye da shekaru goma, na nuna kishin ƙasa da jajircewa wajen yi wa al’umma hidima.

Advertisement

Ta ƙara da cewa idan ya amsa wannan kira, Kano na iya samun sauye-sauye masu ma’ana a fannoni kamar kasuwanci, ababen more rayuwa, bunƙasa matasa da kuma masana’antu.

A ƙarshe, matasan sun buƙaci Little da ya bayyana aniyarsa a hukumance, tare da jaddada cewa suna ganin shi ne ya fi dacewa da jagorantar Kano zuwa wani sabon matakin ci gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending