Connect with us

News

”Na Saci Wayoyi Sama Da 20 Don Sayen Kayan Shaye-shaye” –  Wani Matashi A Kano 

Published

on

Advertisements
Advertisements
Spread the love

Rundunar tsaro ta Anti-Phone Snatching Force (KOSSAP) a Jihar Kano ta cafke wasu matasa ƙananan shekaru da ake zargi da satar wayoyin hannu ta hanyar “sane” a sassa daban-daban na jihar.

Mai magana da yawun rundunar, Ibrahim Garba Ahmad, ya bayyana hakan yayin wata zantawa da manema labaraia ranar Laraba, 25 ga watan Maris, 2026.

Wani Mutum Ya Sace Motar Asibiti Dauke Da Mara Lafiya Da Jami’in Jinya

Advertisement

Ya ce matasan sun dade suna addabar al’umma musamman a yankunan Gidan Zoo, Rijiyar Lemo da kuma wasu kasuwanni, inda suke amfani da dabarar sayar da ruwan leda (pure water) domin kau da hankalin jama’a, kafin su sace wayoyinsu.

A cewarsa, jami’an rundunar ƙarƙashin jagorancin OC Zaman Lafiya, Abdullahi Soja, sun samu nasarar cafke matasan ne bayan wani lamari da ya faru a yankin Gidan Zoo, inda suka sace wa wata budurwa waya da kuɗi daga cikin jakarta.

“Bayan samun rahoto, jami’anmu suka bi sawun su, inda suka kama su tare da ƙwato wayar da kuɗin da suka sace,” in ji shi.

Advertisement

Budurwar da abin ya shafa, Lawisa Nura Hashim, ta bayyana jin daɗinta da yadda jami’an tsaron suka taimaka wajen dawo mata da kayanta, inda ta gode musu bisa ƙoƙarin da suka yi.

A nasa ɓangaren, ɗaya daga cikin matasan da aka kama ya amsa laifinsa, yana mai cewa ya sace wayoyin mutane sama da guda ashirin tun lokacin da ya fara wannan sana’a.

“Na daɗe ina wannan aiki, kuma na sace wayoyi sama da 20. Ina amfani da kuɗin wajen sayen tabar wiwi, sigari da sauran ƙwayoyi, da kuma abinci,” in ji matashin, tare da alƙawarin cewa wannan ne karon ƙarshe da zai aikata irin wannan laifi.

Advertisement

A ƙarshe, rundunar KOSSAP ta yi gargaɗi ga matasa masu aikata irin wannan laifi da su gaggauta daina, tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da cafke duk wanda aka samu da hannu a irin waɗannan laifuka ba tare da sassauci ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending