News
Ta’ammali Da Muggan Kwayoyi Na Daga Cikin Matsalolin Dake Ci Gaba Da Yada Cutar Kanjamau – NDLEA
Hukumar Kula da Hana Sha da Safarar Muggan Kwayoyi ta Kasa NDLEA ta bayyana cewa ta’ammali da muggan kwayoyi na daga cikin motsalolin dake ci gaba da yada cutar Kanjamau a dalilin haka ta yi kira ga gwamnati kan daukan matakan da za su kawar da wadannan matsaloli.
Shugaban Hukumar Buba Marwa ya sanar da haka a taron kaddamar da sabon shiri na yaki da cutar Kanjamau da aka yi a Abuja ranar Laraba.
”Na Saci Wayoyi Sama Da 20 Don Sayen Kayan Shaye-shaye” – Wani Matashi A Kano
Marwa ya ce yaki da ta’ammali da muggan kwayoyi dai-dai yake da yakin da ake yi wajen dakile yaduwar Kanjamau domin yayin da masu ta’ammali da muggan kwayoyi ke amfani da allura wajen Shan kwayar daga nan ne suke iya yada cututtuka musamman Kanjamau a tsakanin su.
Ya kuma ce masu ta’ammali da muggan kwayoyi bayan sun yi mankas da kwaya basa amfani da kariya wajen yin jima’i.
Shugaban hukumar ya kuma ce gidajen yari da gidajen ladabbatarwa na daga cikin wuraren da ake fama da matsalolin ta’ammali da muggan kwayoyi da yaduwar cututtuka.
“Shekaru da dama da suka gabata ana yaki da ta’amali da muggan kwayoyi da yaduwar cututtuka daban-daban amma yanzu mun gano cewa akwai alaka a tsakaninsu da ya kamata a hada hannu domin ganin bayan su.
Marwa ya ce yayin da Hukumar ke bada karfinta wajen hana safarar muggan kwayoyi za ta kara bada karfinta wajen tabbatar da ta hana mutane ta’amali da muggan kwayoyi domin inganta lafiyar mutane.
Ya ce NDLEA za ta hada hannu da Hukumar Dakile Yaduwar Cutar Kanjamau ta Kasa NACA, ma’aikatar lafiya ta Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin Kare Haƙƙin dan Adam domin dakile yaduwar cutar Kanjamau.
Marwa ya ce Hukumar za ta mike tsaye wajen wayar da kan mutane musamman matasa alakar dake tsakanin ta’amali da muggan kwayoyi da yaduwar Kanjamau.
