Connect with us

News

Wani Mutum Ya Sace Motar Asibiti Dauke Da Mara Lafiya Da Jami’in Jinya

Published

on

1774536803118
Advertisements
Advertisements
Spread the love

An shiga rudani a wani babban asibiti a Birtaniya bayan wani mutum ya sace motar asibiti dauke da mara lafiya da jami’in jinya. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:15 na daren Laraba a harabar Royal Stoke University Hospital.

Hukumar ‘yan sanda ta Staffordshire Police ta bayyana cewa nan take ta kaddamar da bincike mai zurfi, inda aka tura jami’ai da kare masu bincike, har ma da amfani da jirgin sama domin bin sawun motar.

Matasa Sun Bukaci Ibrahim Little Ya Tsaya Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC

Advertisement

Motar ta tsaya a wani gidan mai na Esso da ke kan titin A34, a mahadar Liverpool Road da London Road, kusa da yankin Chesterton. Mutumin da ake zargi ya yi ƙoƙarin tserewa, amma jami’an tsaro suka cafke shi.

A cewar jami’in ‘yan sanda, “Mutumin ya shiga motar asibiti da aka ajiye a harabar asibiti ya fice da ita, yayin da a ciki akwai mara lafiya, jami’in jinya da wani mutum.”

Mutumin, mai shekaru 31 daga Stoke-on-Trent, an kama shi bisa zargin garkuwa da mutane, satar mota.

Advertisement

Babu wanda ya samu rauni a cikin motar yayin da aka sace ta. ‘Yan sanda sun bukaci duk wanda ke da bayanai ya kira 101 tare da ambaton lambar rahoto ta 743 na ranar 25 ga Maris.

 

THE MIRROR

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending