News
Jami’an ’Yan Sanda Sun Kama Dilan Miyagun Ƙwayoyi Da Kunshi 879 Na Tabar Wiwi A Kano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi tare da ƙwato kunshi 879 na tabar wiwi a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
An Sallami Jami’an ‘Yansanda 5 Bisa Zargin Garkuwa Da Mutune
Ya ce jami’an rundunar da ke Dawakin Tofa sun gudanar da samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri a ranar 13 ga watan Mayu, 2026, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.
A cewarsa, jami’an sun cafke wani Umaru, wanda aka fi sani da Jalo, mazaunin ƙauyen Yan Shado, yayin da yake sauke buhuna 18 na busassun ganyaye da ake zargin tabar wiwi ce a gidansa.
Sanarwar ta ƙara da cewa binciken da aka gudanar ya kai ga gano kunshi 879 na tabar wiwin da aka ɓoye cikin buhunan.
Rundunar ta bayyana cewa samamen na daga cikin matakan da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ɗauka na ƙara ƙaimi wajen yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da sauran ayyukan ta’addanci a jihar.
CP Bakori ya jaddada cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen murƙushe masu safarar miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa irin waɗannan laifuka na haddasa daba da rashin zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Ya kuma tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ke da hannu a harkar safarar miyagun ƙwayoyin kafin gurfanar da wanda ake zargin a kotu..
