Connect with us

News

Tukin Ganganci Yayin Kai Amarya Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi  ‎

Published

on

Wani matashi mai suna Abubakar Haruna ya rasa ransa a wani mummunan hatsari da ya faru yayin rakiyar amarya a garin Potiskum da ke jihar Yobe.

‎Lamarin wanda ya auku da yammacin ranar Juma’a ya sake jawo hankalin al’umma kan yadda matasa ke gudanar da tukin ganganci a lokutan bukukuwa.

Advertisement

Jami’an ’Yan Sanda Sun Kama Dilan Miyagun Ƙwayoyi Da Kunshi 879 Na Tabar Wiwi A Kano

‎Rahotanni daga shaidun gani da ido sun nuna cewa wasu matasa da ke cikin tawagar rakiyar amarya sun rika tuka babura cikin matsanancin gudu tare da nuna salon tuki mai hatsari a wani yanki mai cunkoson jama’a a garin.

Advertisement

‎An ce yayin da tawagar ke wucewa, ɗaya daga cikin masu baburan ya bugi mamacin da ƙarfi a gefen hanya, lamarin da ya sa ya faɗi cikin wata magudanar ruwa.

‎Ɗan’uwan mamacin, Muhammad Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ‎

Advertisement

‎“Ɗan’uwana yana tsaye ne a bakin hanya lokacin da wani mai babur ya buge shi a kai da ƙarfi. Kafin a kai masa taimako, ya riga ya rasu,” in ji shi.

‎Muhammad ya nuna damuwa kan yadda matasa suka mayar da tukin ganganci wani ɓangare na shagulgula a yankin, yana mai cewa hakan na jefa rayukan jama’a cikin haɗari.

Advertisement

‎“Yanzu duk wani biki sai an yi irin wannan hatsabiban tuki. Rayukan bayin Allah na cikin barazana,” ya ce.

‎Ya kuma yi kira ga hukumomin jihar Yobe da su tsaurara dokokin kiyaye lafiya a hanyoyi tare da hukunta masu karya doka domin dakile aukuwar irin wannan ibtila’i.

Advertisement

‎“Idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, za a ci gaba da rasa rayukan jama’a sakamakon sakaci da rashin bin doka,” in ji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending