News
Jami’an NDLEA Sun Damƙe Wata Tsohuwa Da Hodar Iblis Kilo 13 Da Aka Ɓoye Cikin Bawon Ayaba
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama wata mata ƴar asalin Najeriya mai shekaru 67 da ke zaune a Birtaniya, bisa zargin yunƙurin fasa ƙwaurin hodar iblis mai nauyin kilogram 13 da aka ɓoye cikin bawon ayaba a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
A cewar NDLEA, jami’anta sun gano miyagun ƙwayoyin ne yayin binciken da suka gudanar kan fasinjoji kafin tashin jirgi, inda aka zargi matar da ƙoƙarin safarar hodar iblis ɗin zuwa ƙasashen waje ta hanyar da za ta kauce wa binciken jami’an tsaro.
Gwamnatin Tarrayya Ta Musanta Zargin Ɓoye Kusan Triliyan 9 Don Yaƙin Neman Zaɓen Baɗi
Hukumar ta ce an yi nasarar gano ƙwayoyin ne sakamakon tsauraran matakan bincike da jami’anta ke aiwatarwa domin dakile safarar miyagun ƙwayoyi ta filayen jiragen sama na ƙasar.
NDLEA ta ƙara da cewa bincike kan lamarin na ci gaba domin gano sauran mutanen da ake zargin suna da hannu a wannan haramtacciyar sana’a, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma gurfanar da masu hannu a gaban ƙuliya.
-
News7 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
Uncategorized3 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
