Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Manyan Sakatarori 3 Kan Gano Hukumar Bogi

Published

on

Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin kama wani mutum, Prince George Buchi Nwabueze, bisa zargin hannu wajen kafa wata hukumar bogi a Abuja.

Haka kuma, Shugaban Ƙasar ya dakatar da manyan sakatarori uku a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) dangane da lamarin.

FBI Ta Ce Ba Za Ta Iya Sakin Wasu Bayanan Binciken Shugaba Tinubu Ba

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC), Dokta Musa Adamu Aliyu, SAN, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani bayan ganawarsa da Shugaban Ƙasa ranar Juma’a.

Ya ce an gano wata hukuma mai suna Ofishin Ayyuka na Musamman na Ƙasa, wadda aka kafa ba bisa ƙa’ida ba, a cikin harabar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Manyan sakatarorin da aka dakatar su ne M.S. Danjuma, Injiniya Nadungu Gagare da Richard P. Pheelangwah.

Advertisement

A cewar shugaban ICPC, an gano hukumar ta bogi ne yayin binciken da hukumar ke yi kan wata ƙungiya da ake zargi da kasancewa ta bogi, mai suna Majalisar Tallafawa Harkokin Waje ta Shugaban Ƙasa, wadda Adeyemi Matthew ke gudanarwa.

Dokta Aliyu ya ce binciken ya nuna cewa an bai wa sabuwar hukumar ta bogi ofishi a cikin harabar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, duk da cewa ba ta da hurumin gudanar da ayyukan gwamnati.

Ya ce umarnin Shugaban Ƙasa na kama Nwabueze da dakatar da manyan sakatarorin na daga cikin matakan da aka ɗauka domin zurfafa bincike kan lamarin da kuma gano sauran mutanen da ke da hannu.

ICPC ta ce za ta ci gaba da bincike domin tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu a lamarin ya fuskanci matakin da ya dace.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending