News
‘Yan Ta’adda Sun Ƙona Makarantar Sakandare A Neja
Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun bankawa Makarantar Sakandaren Dekara da ke Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja wuta, watanni biyu bayan sun yi wa al’ummar yankin barazanar cewa za su ɗauki tsauraran matakai idan ba a rufe makarantun yankin ba.
Shugaban makarantar, Malam Zubairu Salihu, ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai, inda ya ce tun a ranar 11 ga watan Mayu, bayan da ‘yan ta’addar suka kai hari garin tare da yin garkuwa da dagacin yankin, sun umarci al’umma da su rufe dukkan makarantu ko kuma su fuskanci mummunan sakamako.
“Ku Yi Aiki Ko Ku Sauka” — Gwamnan Kano Ya Gargaɗi Masu Riƙe Da Muƙaman Gwamnati
Ya ce ƙona makarantar da aka yi na nuna cewa ‘yan ta’addar sun fara aiwatar da barazanar da suka yi wa al’ummar yankin.
Taron manema labaran, wanda Ƙungiyar Ci Gaban Matasan Masarautar Borgu ta shirya, ya mayar da hankali kan neman gwamnatin tarayya da gwamnatin Jihar Neja su gaggauta ɗaukar matakan kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar yankin.
Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar, Abdullahi Yahaya Sadauki, ya ce hare-haren ‘yan ta’adda sun yi kamari matuƙa, inda ya bayyana cewa sama da ƙauyuka bakwai a Masarautar Borgu sun riga sun salwanta sakamakon hare-haren da ake kai wa akai-akai.
Ya ƙara da cewa, watanni uku da suka gabata, ‘yan ta’addar sun tarwatsa gadar Bussa da bam, lamarin da ke kawo cikas ga isa cikin gaggawa da jami’an tsaro ke yi lokacin da aka kai hare-hare.
Abdullahi ya yi kira ga hukumomin gwamnati da su kafa sansanin jami’an tsaro na dindindin a yankin Borgu, yana mai jaddada cewa hakan ne kaɗai zai taimaka wajen dakile yawaitar hare-haren da ke ci gaba da barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
