News
Wasu Bata Gari Sun Hallaka Mai Gadin Asibiti, Sun Sace Kayan Sola A Kano
Wani mai gadin asibiti da ke unguwar Danlasan, a Ƙaramar Hukumar Warawa ta Jihar Kano, Malam Ado Shuaibu Maki, ya rasu bayan wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kai hari, inda suka Hallaka shi tare da sace kayan samar da wutar lantarki ta hasken rana (solar) na asibitin.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a daren Juma’a, 3 ga watan Yuli, 2026, lokacin da ake zargin maharan suka kutsa cikin harabar asibitin, suka kashe mai gadin ta hanyar yanke masa wuya, sannan suka kwashe kayan solar da ake amfani da su wajen samar da wutar lantarki kafin su tsere.
Atiku Ya Zargi Gwamnatin Shugaba Tinubu Da Ɓoye Naira Tiriliyan 8.8 Don Tunkarar Zaɓen 2027
Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Ƙaramar Hukumar Warawa, Malam Hamza Kinchau, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Warawa, Hon. Lamido Sunusi Ahmad, ya nuna matuƙar alhininsa kan wannan mummunan lamari, inda ya jajanta wa iyalan marigayin da al’ummar unguwar Danlasan bisa wannan rashi.
Ya kuma buƙaci hukumomin tsaro da su hanzarta gudanar da bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan ta’asa, tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci hukuncin doka.
