News
Mazauna Dorayi Karama Sun Roƙi Gwamnatin Kano Ta Kawo Musu Ɗauki Kan Matsalar Ambaliyar Ruwa
Mazauna yankin Bayan Gidan Sarkin Dutse Yamma da ke Dorayi Karama a Ƙaramar Hukumar Gwale, sun roƙi Gwamnatin Jihar Kano da sauran hukumomin da abin ya shafa su gaggauta magance matsalar ambaliyar ruwa da suka ce ta addabe su fiye da shekaru 20.
A cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba, 8 ga Yuli, 2026 mai dauke da hannun Dr. Yusuf Ibrahim, mazauna yankin sun bayyana cewa ƙarancin ƙarfin magudanar ruwa ne ke haddasa yawaitar ambaliya a duk lokacin damina, lamarin da suka ce ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi tare da lalata gidaje, hanyoyi da sauran gine-gine.
Sun ce a lokutan ambaliyar ruwa da ta afku a shekarun 2002, 2013 da 2026, wasu daga cikin mazauna yankin sun riƙa toshe bakin magudanar ruwa na wucin gadi domin kare rayukansu da gidajensu daga mamayar ruwa. Sai dai sun jaddada cewa hakan ba don tayar da fitina ko karya doka ba ne, sai don kare kansu bayan sun daɗe ba tare da samun mafita daga hukumomi ba
A cewarsu, abin da ke sa al’umma ɗaukar irin wannan mataki shi ne tsananin wahalar da suke ciki, don haka suka buƙaci hukumomi su fahimci halin da suke ciki tare da mayar da hankali wajen samar da mafita ta dindindin.
Mazauna yankin sun yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwale, Hukumar REMASAB da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da binciken fasaha kan tsarin magudanar ruwan yankin, su kira taron dukkan al’ummomin da abin ya shafa domin cimma matsaya, sannan su gina ko inganta babbar magudanar ruwa mai isasshen ƙarfi domin kawo ƙarshen matsalar.
Sun kuma jaddada cewa suna goyon bayan zaman lafiya da bin doka da oda, tare da yin kira ga matasan yankin su ci gaba da kasancewa masu haƙuri da kauce wa duk wani abu da zai iya haddasa tashin hankali.
Mazauna yankin na fatan hukumomi za su gaggauta ɗaukar matakin da zai kawo ƙarshen matsalar ambaliyar ruwa da ke addabarsu.
-
News2 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News3 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News3 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
