Connect with us

Uncategorized

Kano First Forum Ta Kai Ƙorafi Ga Ƴansanda Kan Kalaman Aminu Babba Dan Agundi

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,

Ƙungiyar Kano First Forum ta kai ƙorafi ga Kwamishinan Ƴansandan Jihar Kano kan wasu kalaman da ta ce Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya yi, waɗanda ƙungiyar ke ganin ka iya ƙara dagula zaman lafiya da haifar da tashin hankali a jihar.

A cikin ƙorafin da lauyoyin ƙungiyar suka shigar, Kano First Forum ta nemi rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta gudanar da cikakken bincike cikin sirri da adalci domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma yanayin kalaman da ake zargin Dan Agundi ya yi.

Haɗurran Ababen Hawa Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane  1,347 Cikin Watanni Uku —Rahoto

Ƙungiyar ta ce kalaman sun fito ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar 1 ga Oktoba, 2026, bayan halartar Khalifa Muhammadu Sanusi II, Sarkin Kano, bikin ranar samun ’yancin kan Najeriya.

A cewar ƙorafin, taron manema labaran ya ta’allaka ne, a tsakanin sauran batutuwa, kan batun amfani da doki da Sarkin ya yi a yayin bikin, duk da cewa akwai umarnin gwamnatin Jihar Kano da ya shafi amfani da dawakai.

Sai dai abin da ya fi jawo hankalin ƙungiyar shi ne wani furuci da ta ce an danganta wa Dan Agundi, inda ake zargin ya ce al’ummar Kano su “jira dawowarsu, su kuma jira ƙarin umarni daga gare su”.

Advertisement

Kano First Forum ta ce ta ɗauki wannan furuci da muhimmanci ne saboda rikice-rikicen da aka dade ana samu dangane da masarautar Kano, tana mai cewa ya kamata a yi taka-tsantsan da kalaman da za su iya haifar da shakku ko ƙara tayar da hankalin jama’a.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ƙorafinta ba wai ya shafi bambance-bambancen siyasa ko na masarauta kawai ba ne, sai dai damuwarta ta ta’allaka ne kan abin da ka iya biyo bayan wasu kalamai a yanayin da ake ciki.

Ta ce barin jama’a cikin rashin tabbas kan wanda ake nufi da “dawowa”, abin da dawowar za ta ƙunsa da kuma ma’anar “ƙarin umarni” na iya haifar da fargaba da tashin hankali ba tare da wata fa’ida ba.

 

Saboda haka, ƙungiyar ta ce ta garzaya ga ƴansanda ne domin a dauki matakan da suka dace na hana duk wani abu da ka iya ƙara dagula yanayin da ake ciki.

 

Advertisement

Sai dai Kano First Forum ta jaddada cewa matakin nata ba yunƙurin hana mutane bayyana ra’ayinsu, yin suka ko gudanar da muhawara bisa doka ba ne.

 

A maimakon haka, ta ce burinta shi ne ganin an magance dukkan batutuwan da suka shafi masarautar Kano ta hanyoyin doka da zaman lafiya, ba tare da jefa rayukan al’umma cikin hatsaniya ko barazanar rikici ba.

 

Ƙungiyar ta bukaci rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta binciki lamarin tare da duba yanayin da aka furta kalaman, domin tantance ko sun karya wata doka ko kuma suna da damar kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a.

 

Advertisement

Haka kuma, ta yi kira ga ’yan siyasa, sarakuna, malaman addini da shugabannin al’umma da su riƙa taka-tsantsan wajen yin kalamai a bainar jama’a, musamman kan batutuwan da suka shafi masarautar Kano.

 

Kano First Forum ta ce Kano muhimmiyar jiha ce ta fuskar kasuwanci, zamantakewa da siyasa, don haka zaman lafiyarta na da muhimmanci ga miliyoyin mutane a ciki da wajen jihar.

 

“Duk wani saɓani da ake da shi kan masarautar Kano, ya kamata a warware shi ta hanyar kotuna da sauran hukumomin da doka ta tanada, ba ta hanyar kalaman da za a iya fassara su a matsayin barazana, umarni ko kira ga yin fito-na-fito ba,” in ji ƙungiyar a cikin ƙorafinta.

 

Advertisement

Ta ce za ta ci gaba da mara wa zaman lafiya, tsaron jama’a da bin doka baya, tana mai cewa ƙorafin ya samo asali ne daga buƙatar kauce wa duk wani rikici da za a iya hana shi tun kafin ya faru.

 

An aika kwafin ƙorafin ga Sufeto-Janar na Ƴansanda na ƙasa da kuma Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) domin su samu damar duba lamarin.

 

Ƙungiyar ta kuma bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin tare da ɗaukar matakin da doka ta tanada, idan binciken ya nuna cewa akwai abin da ya dace a yi, domin kare zaman lafiya da tsaron jama’a a Jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending