News
Lagos, Kano, Kaduna Na Kan Gaba Wajen Yawan Masu Rajistar Zaɓe – INEC
Jihohin Lagos, Kano da Kaduna ne suka fi yawan masu rajistar zaɓe a Najeriya, yayin da ake tunkarar babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027, kamar yadda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce adadin masu rajistar zaɓe a faɗin ƙasar ya kai sama da miliyan 110.
NAF Ta Fitar Da Sunayen Mutane 25 Da Suka Mutu A Haɗarin Jirgin Soji
A cewar hukumar, Lagos ce ke kan gaba da masu rajistar zaɓe 7,488,633, sai Kano mai 6,570,276, yayin da Kaduna ke matsayi na uku da masu rajista 4,662,640.
Katsina ce ke matsayi na huɗu da 3,876,051, sai Rivers da 3,736,434, Oyo da 3,588,111, Delta da 3,525,988, Benue da 3,057,225, da Ogun mai 3,037,981.
Jihar Bauchi ce ta cika jerin jihohi 10 da suka fi yawan masu rajistar zaɓe, inda take da mutane 3,012,547 da aka yi wa rajista.
Amupitan ya bayyana cewa alkaluman sun ƙunshi bayanan rajistar masu zaɓe da hukumar ta tattara daga matakai uku na aikin rajistar.
