Connect with us

News

Cutar Mashaƙo Ta Yi Ajalin Yara Biyar ‘Yan Gida Daya Cikin Mako Guda A Kano

Published

on

IMG 20261009 110243 226

Wani mutum mai suna Ibrahim Yusuf, mazaunin Danbare a Kano, ya ce ya rasa ’ya’yansa biyar cikin kwanaki takwas sakamakon zargin kamuwa da cutar mashako.

Y a ce yaran sun fara fama da zazzaɓi a makon da ya gabata, inda aka kai su Cibiyar Lafiya ta Farko ta Kabuga, daga bisani aka tura su Asibitin Cututtuka Masu Yaɗuwa (IDH).

Kotu Ta Yi Watsi Da Karar El-Rufai Ta Neman Hana DSS, EFCC da ICPC Dakatar Da Asusunsa Da Kwace Kadarorinsa

A cewarsa, biyu daga cikin yaran sun rasu ranar Litinin, yayin da sauran ukun suka rasu a ranakun Talata da Laraba. Marigayin yaran sun haɗa da Sadiq mai shekara 13, Aisha da Zainab masu shekara 7, Umar mai shekara 6, da Aliyu mai shekara ɗaya da wata shida.

Ibrahim, wanda yake da ’ya’ya 11, ya roƙi gwamnati ta taimaka wajen dakile cutar da kuma tallafa wa iyalansa.

Wani ma’aikacin Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Kano (KNCDC) ya tabbatar da mutuwar yara biyar a wani cibiyar lafiya, yana mai cewa adadin mace-macen na ƙaruwa.

Advertisement

Hukumar ta ce tun daga shekarar 2022, an samu sama da mutane 38,000 da ake zargin sun kamu da cutar a Kano, inda sama da 31,000 aka tabbatar sun kamu kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending