News
Gwamnatin Kano Ta Kashe Naira Biliyan 2.7 Kan Talla Na Kakafen Yaɗa Labarai, Da Alawus A Watanni Shida
Rahoton kasafin kuɗin jihar Kano na zangon farko da na biyu na shekarar 2026 ya nuna cewa gwamnatin jihar ta kashe kusan naira biliyan 2.7 kan tallace-tallace, talla na kakafen yaɗa labarai, da alawus na zaman taro tsakanin watan Janairu da Yuni.
Rahoton ya nuna cewa an kashe naira biliyan 1.49 kan tallace-tallace, yayin da aka kashe naira biliyan 1.207 kan talla na kakafen yaɗa labarai, da alawus na zaman taro.
Kansilar Da Aka Sace Ta Rasu A Hannun Waɗanda Suka Sace Ta A Kogi
Wannan kuɗi na daga cikin naira biliyan 10.36 da gwamnatin jihar ta kashe kan wasu kuɗaɗen gudanarwa a farkon rabin shekarar.
A bangare guda, kuɗin da aka kashe kan shirin tallafin karatu a ƙasashen waje ya kai naira miliyan 162.95, daga cikin naira biliyan 26.23 da aka ware wa shirin a kasafin shekarar 2026.
