Connect with us

Labarai

Abin Da Na Faɗa Kan Naɗar Hirar Ribaɗu Ba  Gaskiya Ba Ne Zolayace Irin Ta Siyasa – —El-Rufa’i Ga kotu

Published

on

mallam nasir el rufai governor of kaduna state nigeria
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Tsohon gwamnan Kaduna da yanzu ya ke a tsare bisa zargin cin hanci da rashawa, Nasiru El-Rufa’i, ya ce zolayace irin ta siyasa ta sa yace ya na yi wa tarho din Nuhu Ribaɗo, mai bai wa Shugaban ƙasa shawara ta fuskar tsaro laɓe, amman sam ba da gaske ya ke ba.

Tsohon gwamnan ya furta hakan ne yayin da ake mai tambayoyin ƙwaƙwa a shari’ar da ya ke fuskanta da hukumomin tsaron Najeriya kan iƙirarin nasa.

Jami’an NDLEA Sun Kama Wasu Ƴan Ƙasar Mexico Dake Sarrafa Muggan Ƙwayoyi A Najeriya

A yayin tambayoyin bada bayanan shedar, wanda babban lauyansa Paul Erokoro, SAN, ya jagoranta, El-Rufa’i ya ce shi ko iya yadda ake wa tarho laɓe ma bai sani ba, ballantane ya mallaki na’u’rorin bibiyar maganganun mutane a wayar tarhon.

A don haka tsohon gwamnan ya ce ya yi kalaman nasa ne da nufin cusawa gwamnati haushi da sa ta jin irin raɗaɗin da su ma su ke ji.

Tun a watan Fabrairun 2026 ne dai, Nasiru El-Rufa’i ya yi wata hira a talbijin ɗin Arise, inda ya yi iƙirarin cewar su na bibiyar wayar tarho din Babban mai bai wa Shugaban ƙasa shawara ta fuskar tsaro, Nuhu Ribaɗo don jin maganganun da ya ke ƙullawa, iƙirarin da hukumomin tsaron ƙasa su ke wa kallon babban laifi ne da ke iya haifar da tarnaƙi ga bayanan sirrin tsaron ƙasa. A kan haka ne, gwamnatin Najeriya ta gurfanar da shi a gaban kotu.

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending