Connect with us

Labarai

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Wani Matashi Kan Zargin Hallaka wani dattijo mai shekara 70 da Kibiya

Published

on

1000084111.jpg
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta kama wani matashi mai shekara 18, Shadrack Tizhe, bisa zargin kashe wani dattijo mai shekara 70, Zubairu Bayi, a ƙaramar hukumar Mubi ta Arewa.

Sanarwar rundunar ta ce a ranar 24 ga Nuwamba, 2026, an samu rahoton cewa wanda ake zargin ya kai wa dattijon hari da baka da kibiyoyi a yankin Wuro Barka, lokacin da yake dawowa gida daga wani daji da ke kusa, lamarin da ya sa ya faɗi.

Adadin ‘Yan Najeriya Da Amurka Ke Shirin Kora Ya Kai 157

’Yan sanda sun ce bayan isar jami’ansu wurin, sun tarar da dattijon a sume, inda aka garzaya da shi asibiti, amma likita ya tabbatar da rasuwarsa. An kama wanda ake zargin, tare da ƙwato baka da kibiyoyin da ake zargin an yi amfani da su wajen kai harin.

Kwamishinan ’Yan Sandan Adamawa, CP Kabir Umar Hassan, ya umarci sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) da ke Yola da ya karɓi binciken domin gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da wanda ake zargin. Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su guji tashin hankali, su riƙa warware saɓani ta hanyoyin doka da lumana.

 

Advertisement

DAILY POST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending