Labarai
BAYAN WATA SHIDA: Shugaba Tinubu Ya Yi Alƙawarin Kuɓutar da Ɗaliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Borno

Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da kuɓutar da ɗaliban da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Askira-Uba ta Jihar Borno, waɗanda suka shafe kusan watanni shida a hannun ƴan ta’adda.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Abin Da Na Faɗa Kan Naɗar Hirar Ribaɗu Ba Gaskiya Ba Ne Zolayace Irin Ta Siyasa – —El-Rufa’i Ga kotu
Shugaban ya ce yana da yakinin cewa haɗin gwiwar rundunar sojin ƙasa da hukumomin leƙen asiri zai taimaka wajen gano inda yaran suke tare da kuɓutar da su cikin aminci.
Ya ce: “Yaran da aka yi garkuwa da su a Askira-Uba suna cikin addu’o’inmu, kuma rundunar sojojinmu da hukumomin leƙen asiri suna ƙoƙari. Za mu kuɓutar da su, insha Allah.”
Tinubu ya kuma yabawa jami’an tsaro da ke gudanar da ayyukansu cikin mawuyacin yanayi domin dawo da zaman lafiya a Jihar Borno, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Sai dai wannan tabbaci na shugaban ƙasar ya zo ne yayin da iyalan yaran ke ci gaba da nuna damuwa kan tsawon lokacin da suka ɗauka ba tare da samun labarin halin da ƴaƴansu suke ciki ba.
Rahotanni sun nuna cewa an sace aƙalla yara 42 a garin Mussa na ƙaramar hukumar Askira-Uba a ranar 15 ga watan Mayun 2026, yayin da aka sake yin garkuwa da wasu yara 36 a garin Lassa da ke ƙaramar hukumar a ranar 29 ga watan Yunin 2026.
Jimillar yaran da aka yi garkuwa da su sun kai 78, ciki har da ƙananan yara masu shekaru biyu da kuma wasu da ke ƙarƙashin kulawar iyayensu.
Shugaban ƙungiyar iyayen yaran, Ishaku Suya, ya nuna rashin gamsuwarsa da sabon alƙawarin shugaban ƙasar, yana mai cewa iyalan sun shafe watanni shida suna jiran matakin da zai kai ga kuɓutar da ƴaƴansu.
Ya ce gwamnati ta sha yin alƙawarin ceto yaran, amma har yanzu ba a samu wani sakamako na zahiri ba.
