Connect with us

Labarai

Rundunar Anti-Phone Snatching Ta Kama Matashi Mai Shekaru 21 Kan Zargin Sayar Da Ƙwayoyi Da Tabar Wiwi A Kano

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Rundunar yaƙi da faɗan daba, ƙwacen waya da safarar miyagun ƙwayoyi ta Anti-Phone Snatching Force a Kano, ta kama wani matashi mai suna Yusuf Abdullahi, mai shekaru 21, bisa zargin sayar da ƙwayoyi da tabar wiwi a yankin Fagge da ke jihar.

Kwamandan rundunar a Kano, CMD Nura Salisu Sharada, ne ya bayyana hakan ga gidan rediyon Dala FM Kano a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, 2026.

Hare-Haren Siyasa 124 Sun Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 22 Cikin Watanni Huɗu — Rahoto

Ya ce an kama matashin ne tare da ƙwayoyin Exsol guda 350 da kuma kofuna 10 na tabar wiwi, waɗanda ake zargin yana sayarwa a yankin ƙaramar hukumar Fagge.

A cewarsa, rundunar ta samu bayanan sirri kan yadda wasu matasa ke harkar sayar da miyagun ƙwayoyi da tabar wiwi, lamarin da ya sa ya tura jami’ansa na rundunar ‘Damisa Ƙi Sabo’ domin gudanar da samame.

Ya bayyana cewa jami’an sun yi nasarar tarwatsa wasu daga cikin waɗanda ake zargin suna gudanar da harkar, tare da kama Yusuf Abdullahi.

Advertisement

Kwamandan ya ƙara da cewa a halin yanzu ana gudanar da bincike kan wanda ake zargin, kuma da zarar an kammala, za a miƙa shi ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar matakin doka.

Da yake nasa bayanin ga Dala FM, matashin ya ce rashin samun tallafi daga wasu ‘yan siyasar da ya yi wa hidima a baya ne ya jefa shi cikin harkar sayar da miyagun ƙwayoyi.

Ya bayyana cewa ya shiga wannan sana’a ne domin samun kuɗin abinci da kuma taimaka wa mahaifiyarsa da ƙanwarsa.

Yusuf ya kuma nuna takaicinsa kan yadda mutanen da ya kira masu gidan siyasarsa suka gaza taimaka masa wajen samun kuɗin tiyatar da yake buƙata, sakamakon wata lalura da ta shafi wani ɓangare na jikinsa.

Ya ce wannan hali ya sa yake nadamar irin gudunmawar da ya bayar a harkokin siyasar da ya shiga a baya.

A nasa ɓangaren, Nura Sharada ya gargaɗi dukkan masu aikata laifuka da ke addabar al’umma da su daina, yana mai cewa rundunar ba za ta yi sassauci ga duk wanda ta kama da laifi ba.

Advertisement

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin yaƙi da aikata laifuka domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a faɗin jihar Kano.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending