Connect with us

News

Abu biyar da ake tunanin na karya azumi amma ba sa karyawa —Sheikh Jabir Sani MaiHula

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Sannanen malamin addini Sheikh Jabir Sani MaiHula a wata zantawa da BBC Hausa Ta Yi da shi ya fayyace wasu abubuwa da ake gani idan mai azumi yayi kamar azumin sa ya sami tazgaro to amma zurfin bincike da karatu yasa an gano sam basu da illa.

Advertisement

Malamin yace akwai abubuwa kimanin guda biyar da basa karya azumi amma a rashin fahimta sai ana musu kallon suna da illa ga azumi.

A Daina Zancen Kabilanci Da Kalaman Kiyayya – Miyatti Allah- (MACBAN) 

Abu na farko akwai amfani da man wanke baki wato ‘Tooth paste’inda yace malamai irin su Bimbaz sun yi fatawar cewar ba ya karya azumi saboda ba abin ci ba ne kuma ba abin sha bane,Saboda ba ya larabawa zuwa cikin mutum.

Advertisement

Ba da Jini ga mabuƙata shima baya karya azumi

Abu na gaba akwai allura malamin ya ce tabbas yin allura ba ya lalata azumi in Har ba allurar abinci ba ce ko ta abin sha.

Advertisement

Sannan inhaler ma ba ta karya azumi wato abun shakar numfashi itama bata karya azumi masu cutar athma ko kuma lalura na mura in mutum yayi amfani da ita azumin sa na nan ko da kuwa kaji maƙaƙin sa a maƙoshi.

Malamin ya ƙara da cewa abu na gaba da baya karya azumi shi ne maganin ciwon ido wanda ake ɗigawa ba ya karya azumi ko da kuwa mutum ya ji shi a maƙoshin sa

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending