Connect with us

News

Jami’an Hukumar EFCC Sun Gurfanar Da Manajan Darakta Kan Damfarar Kudade A Gombe

Published

on

DAGA MAIMUNA RABIU UMAR 

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), reshen jihar Gombe, ta gurfanar da Shugaba kuma Manajan Darakta na kamfanin MB Lugga Global Travels and Tours Limited, Mustapha Mohammed, a gaban kotu bisa zargin damfarar Naira miliyan 144 ta hanyar yin karya da kwace kuɗi da gangan.

Advertisement

An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban mai shari’a T.G. Ringim na babbar kotun tarayya da ke Gombe, bisa zargin karɓar wannan adadin daga Hamza Ibrahim Maina da Ibrahim Arabia domin shirya tafiyar Umrah a lokacin azumin Ramadana na 2024.

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ta dakatar da amfani da shafukan X da Tiktok

A cewar tuhuma ta farko, Mohammed ya haɗa kai da wani Nazifi Sale Idris, wanda har yanzu ba a kama ba, don karɓar N97,080,000 daga Hamza Ibrahim Maina ta asusun bankinsa na Access Bank domin siyan tikitin jirgi, biza da masauki don tafiya Umrah. Sai dai, wanda ake tuhuma bai cika alƙawarin da ya yi ba, lamarin da ya saba wa sashi na 1(1)(a) na dokar hana damfara ta 2006.

Advertisement

Lauyan EFCC, S. H. Sa’ad, ya nemi kotu ta sanya rana don fara shari’a tare da bukatar a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali na Gombe. Sai dai lauyan wanda ake tuhuma, M.Z. Gambo, ya nemi belinsa, wanda lauyan gwamnati ya ƙi amincewa da hakan.

Mai shari’a Ringim ya ɗage sauraron shari’ar zuwa wani lokaci don yanke hukunci kan buƙatar beli, tare da bada umarni cewa a ci gaba da tsare Mustapha Mohammed a gidan gyaran hali na Gombe har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADSHIP

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending