Connect with us

News

Jami’an ICPC  Binciki Gidan El-rufai Da Ke Abuja

Published

on

mallam nasir el rufai governor of kaduna state nigeria

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa mai suna ICPC ta binciki gidan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke Abuja a ranar Alhamis.

Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X (tsohon Twitter).

Advertisement

Gwamnatin Yobe Ta Dakatar Da Dokar Takaita Zirga-zirga Albarkacin Ramadan

Da yake mayar da martani, lauyan El-Rufai, Ubong Akpan, ya bayyana matakin a matsayin wanda ya saɓa wa doka tare da keta haƙƙin ɗan adam na abokin aikinsa. Bai bayyana ko an kwashe wasu kayayyaki daga gidan ba.

Advertisement

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ICPC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin.

Binciken na ICPC ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da daukar matakai daga hukumomin tsaro kan tsohon gwamnan.

Advertisement

A ranar Litinin, EFCC ta tsare El-Rufai bisa zargin almundahana. An sake shi da misalin karfe 8:00 na dare a ranar Laraba, amma nan take jami’an ICPC suka kama shi a hedikwatar EFCC da ke Abuja.

Har yanzu ICPC ba ta yi bayani a fili ba kan binciken gidansa.

Advertisement

A wani bangare na daban, hukumar SSS ta shigar da ƙarar laifin yin kutse a kan El-Rufai a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Ana zargin sa da karya dokar sadarwa bayan wasu kalamai da ya yi a wata hira kai tsaye a shirin “Prime Time” na Arise Television a makon da ya gabata.

Advertisement

A hirar, El-Rufai ya yi zargin cewa an saurari wayar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, kuma ya ce ya ji umarnin a kama shi.

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending