News
Gwamnatin Yobe Ta Dakatar Da Dokar Takaita Zirga-zirga Albarkacin Ramadan
Gwamnatin Jihar Yobe ta sanar da ƙarfafa matakan tsaro a faɗin jihar, tare da sassauta dokar hana zirga-zirga da tsakar dare domin bai wa Musulmi damar gudanar da ibadun watan Ramadan cikin kwanciyar hankali.
Mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar mai ritaya Dahiru Abdussalam, ne ya bayyana hakan bayan taron kwamitin tsaro na wata-wata da aka gudanar a Damaturu.
Gobarar Singa Ta Sanya Fargabar Tashin Kayan Masarufi A Ramadan
Ya ce kwamitin tsaron ya sake duba halin da ake ciki na tsaro, inda aka amince da ƙarfafa matakan kariya domin dakile duk wata barazana, musamman a lokacin sallar dare.
A cewarsa, jami’an tsaro sun ƙara sintiri da sa ido, tare da tattara bayanan sirri a manyan garuruwa da wuraren da ake ganin na iya zama matsala. Haka kuma, an tura jami’ai wurare masu muhimmanci domin hana fashi da sauran laifuka a lokutan da jama’a ke fita ibada.
Abdussalam ya ce an kuma wayar da kan malamai da shugabannin addini domin su ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kan al’umma.
Ya bayyana cewa sassauta dokar hana zirga-zirga da dare zai bai wa mazauna damar halartar Tafsiri da sauran ibadun dare har zuwa wayewar gari.
Sai dai ya buƙaci al’umma su ba jami’an tsaro haɗin kai, tare da bin duk wasu ƙa’idojin da aka shimfiɗa a wasu wurare.
Game da takaita zirga-zirga a hanyar Family Support Roundabout zuwa Ali Marami Housing Estate a Damaturu, ya roƙi jama’a su yi haƙuri, yana mai cewa matakin na wucin gadi ne saboda dalilan tsaro, kuma za a sake dubawa idan al’amura sun daidaita.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
