News
Gwamnatin jamhuriyar Nijar Ta Haramta Ɗaukar Hoton Waɗanda Aka Baiwa Tallafi Da Ramadana
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta sanar da haramta ɗaukar hotunan marasa ƙarfi da ake taimakawa da kayan abinci lokacin azumin Ramadan tare da watsa su a kafafen sada zumunta.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta fitar, ta ce daga yanzu babu wata ƙungiya da ke taimakawa mabuƙata da aka baiwa damar ɗaukar hotunan mutane tare da yaɗa su a duniya.
A cewar sanarwar, yin hakan cin zarafin mabuƙata ne, da kuma jefa su cikin haɗari don haka daga yanzu hakan ba zata sake faruwa ba, musamman daga ƴan ƙungiyoyi.
Bisa al’ada dai akan ga yadda wasu ɗai-ɗaikun mutane da kuma ƴan ƙungiyoyi na ɗauka da kuma yaɗa hotuna ko kuma Bidiyon mutanen da suka taimakawa musamman lokacin azumin Ramadan.
Wannan na jefa mutuntaka da tsaron mutanen cikin haɗari, yayinda ake zargin ƴan ƙungiyoyin na amfani da hotunan ta wata hanya daba don neman kudi ko kuma wata biyan buƙata ta daban.
-
News20 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
