Connect with us

News

Shugaban Tashar Dala FM Kano, Ahmad Gazzali Yakub , Ya Yi Murabus Daga Aikinsa ‎

Published

on

IMG 20260226 195025 330

Shugaban tashar Dala FM Kano, Ahmad Gazzali Yakubu, ya ajiye aikinsa daga rukunin tashoshin Freedom Radio Nigeria bisa raɗin kansa.

Ahmad Gazzali Yakubu, wanda aka fi sani da Baba Gaza, na daga cikin ma’aikatan farko-farko na Freedom Radio, inda ya shahara wajen gabatar da shirye-shiryen siyasa, labarai da rahotanni da suka shafi al’amuran yau da kullum.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Kwato Motocin Tsaffin Kwamishinonin Da Suka Yi Murabus ‎

Ya kuma gabatar da shirye-shirye da dama da suka samu karɓuwa, ciki har da shirin Kowanne Gauta, wanda ake watsawa a tashoshin Freedom Radio.

Advertisement

Jajircewarsa da ƙwarewarsa ne suka sa aka ba shi shugabancin Dala FM — tashar da ta fi mayar da hankali kan al’amuran matasa, mata da kuma zaurukan al’umma. A lokacin jagorancinsa, tashar ta ƙara samun karɓuwa a tsakanin masu sauraro.

Wasu ma’aikatan tashar sun bayyana kaduwarsu da barin aikinsa, suna mai cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen kula da walwalar ma’aikata da kuma horas da sabbin ‘yan jarida da dama.

Advertisement

Rahotanni sun ce, yayin da yake bankwana da ma’aikatansa, ya yi musu fatan samun shugabanci nagari da zai ɗora daga inda ya tsaya, tare da yi musu fatan alheri a ayyukansu na gaba..

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending