Connect with us

News

‎An Kama Jami’an Gwamnatin Ghana 9 Da Kwantena Dauke Kwayoyin Tramadol

Published

on

IMG 20260306 062140 018

Jami’an tsaro a ƙasar Ghana sun kama jami’an gwamnati guda tara bisa zargin hannu a wani lamari da ya shafi kwantena mai ɗauke da dimbin kwayoyin tramadol da ba a bayyana su ba a tashar jiragen ruwa ta Tema.

Daga cikin jami’an gwamnatin da aka damke, biyar ma’aikatan kwastam ne da kuma guda daga hukumar dake yaki da safarar miyagun kwayoyi, jami’in tsaron tashar jiragen ruwa, jami’i daga Hukumar Makamashi, da kuma jami’i daga Hukumar Ingancin Kaya ta Ghana.

Advertisement

Jami’an Yansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Yada Sakon Tunzuri Ga Jama’a A Kano

‎A wata sanarwa da Hukumar Tara Haraji ta Ghana (GRA) ta fitar, ta ce kama jami’an ya biyo bayan cafke Wata kwantena da ke ɗauke da kartuna 299 na kwayoyin tramadol hydrochloride da ba a bayyana su ba.

Advertisement

‎Hukumar ta ce jimillar kwayoyin da aka gano sun kai 146,932,000, masu karfin 250mg da 225mg, tare da nauyin da ya kai kilogiram 34,847.2.

An tsare kwantenan mai lamba TGHU6228715 a ranar 26 ga Fabrairu, 2026, kafin a kai shi wurin ajiyar Kwastam domin ƙarin bincike a tashar jiragen ruwa ta Tema.

Advertisement

‎Rahoton ya ce kayan sun fito ne daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), inda a takardun shigo da kayan aka bayyana su a matsayin kayan amfanin gida, ciki har da tukwanen dumama ruwa, injinan niƙa na kicin, baƙin ƙarfe, fitilun rage amfani da wuta da kuma kayan roba.

‎Sai dai yayin wani sake bincike da jami’an Kwastam tare da tawagar sa ido kan kudaden shiga suka gudanar a ranar 1 ga Maris, 2026, an gano cewa an ɓoye dimbin kwayoyin tramadol a cikin kwantenan tare da wasu daga cikin kayan da aka bayyana.

Advertisement

‎Hukumar ta ce an miƙa mai shigo da kayan da kuma wanda ya cike takardun shigowar ga ’yan sanda domin taimakawa bincike da ake ci gaba da yi.

‎A cewar GRA, har yanzu kwantenan da kwayoyin da aka kama na karkashin kulawar Kwastam, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike kan lamarin.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending