News
Jami’an Yansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Yada Sakon Tunzuri Ga Jama’a A Kano
Rundunar ƴansandan Jihar Kano ta sanar da kama wani mutum da ake zargi da yaɗa saƙonnin bidiyo da murya masu tayar da hankali da ka iya haddasa rikici da firgita mazauna jihar.
A wata sanarwa da kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya fitar a ranar 5 ga Maris, 2026, ya bayyana cewa rundunar ta gano yadda ake yaɗa saƙonnin a kafafen sada zumunta, inda ake zargin suna ɗauke da kalamai masu tunzura jama’a da ka iya haddasa rashin zaman lafiya.
Gwamnatin Lagos Ta Kama Mutane 275 Saboda Yin Bahaya A Waje
Sanarwar ta ce rundunar ta gudanar da wani samame na musamman inda ta samu nasarar kama wanda ake zargin, kuma a halin yanzu ana yi masa tambayoyi domin ci gaba da bincike
Rundunar ta jaddada cewa tana ɗaukar irin waɗannan kalamai masu tunzura jama’a da matuƙar muhimmanci, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
