Connect with us

News

Gwamnatin Lagos Ta Kama Mutane 275 Saboda Yin Bahaya A Waje 

Published

on

ce55e3a52e3b0bcf43505b8bbc6e97152a58e04095e0ce71a349d76013d52a3b 768x576

Gwamnatin Jihar Lagos ta kama mutane 275 a sassa daban-daban na jihar saboda yin bahaya a waje, duk da cewa akwai bandakunan  jama’a da Gwamnatin ta gida guda 8,710 da ke aiki.

‎Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa, Tokunbo Wahab, ya ce an yi waɗannan kamun tun daga ranar 1 ga Janairu. Ya bayyana cewa mutane kusan 70 ne aka kama a Tsibirin Lagos, 62 a Berger, yayin da wasu 43 aka kama a Oshodi suna yin bahaya a waje.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Wa’adin Shekaru Shida Kafin Kafa Sabbin Manyan Makarantu A Najeriya

‎“Yin bahaya a waje laifi ne. Muna da bandakuna masu aiki a duk fadin jihar, ciki har da gidajen abinci da tashoshin mota,” in ji Wahab.

Advertisement

‎Ya ƙara da cewa akwai ƙungiyar yaki da yin bahaya a waje wacce ke yawo kowace rana, musamman karfe 3, 6, da 7 na safe, don hana wannan dabi’a. “Muna kama masu laifi mu kai su kotu a kullum.

‎A shekarar 2024, Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Lagos tare da ta Jihar Ogun sun kaddamar da shiri domin kawo ƙarshen yin bahaya a waje a kan hanyar Lagos–Ibadan Expressway.

Advertisement

‎ Wannan na nufin kare lafiya da tsaftar muhalli, da rage yaduwar cututtuka kamar sankarau.

‎Rahoton UNICEF na 2022 ya nuna cewa rashin tsafta na kashe yara sama da 100,000 a Najeriya duk shekara, musamman saboda gudawa da rashin ruwa mai tsafta.

Advertisement

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending