News
RIKICIN AMURKA DA IRAN: Tsadar fetur Ta Tilastawa Direbobi A Kano Ajiye Motocin
Rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka da Israila a kan Kasar Iran tun cikin watan Fabrairu, 2026 na ci gaba da haifar da tasiri a rayuwar al’umma a sassa daban-daban na duniya, ciki har da Najeriya. A birnin Kano, masu ababen hawa na fuskantar ƙarin tsadar man fetur, lamarin da yake ci gaba da sauya salon rayuwarsu.
Rahotanni daga yankin Gabas ta Tsakiya suna nuni da cewa tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya ya faru ne saboda wannan yaki, yayin da farashi ya haura dala 100 a kowace ganga.
Wakilanmu sun gano cewa, rikicin ya janyo karin farashin fetur a ƙasashe da dama har da Najeriya.
A Najeriya, matatar mai ta Dangote ta ƙara farashin fetur saboda halin da aka shiga, tana danganta hakan da halin da ake ciki a kasuwar duniya.
A Kano, lamarin ya haifar da raguwar zirga-zirgar ababen hawa, yayin da wasu masu motoci suka ajiye su saboda tsadar mai. Hakan ya sa jama’a da dama suka koma amfani da A Daidaita Sahu, babura ko kuma tafiya da ƙafa domin biyan bukatun yau da kullum.
Farashin litar fetur a wasu gidajen mai yana tsakanin naira 1,300 zuwa 1,320, abin da ke ci gaba da jefa masu ababen hawa cikin ƙunci. Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa ba za su iya ɗaukar nauyin sayen mai a irin wannan farashi ba, musamman a yanayin da ake fama da tsadar rayuwa.
Wani ɗan kasuwa a Kano ya shaida cewa ya daina amfani da motarsa, yana koma shiga abin hawa na haya saboda rage kashe kuɗi. Haka zalika, wasu iyaye sun ce sun daina kai ‘ya’yansu makaranta da mota, suna ba su kuɗin haya ko kuma su tafi da ƙafa a wani lokacin.
A gefe guda, wasu sun koma amfani da babura ko kekuna a matsayin mafita. Wani ma’aikacin gwamnati ya bayyana cewa ya sayar da motarsa domin sayen babur, yana mai cewa hakan ya fi sauƙi wajen sayen mai.
Wannan lamarin ya haifar da muhawara a kan amfani da iskar gas (CNG) a matsayin madadin man fetur a cikin ababen hawa. Sai dai kuma, masu ababen hawan na ci gaba da nuna damuwarsu a kan tsadar sauya injin mota ya zuwa mai amfani da gas, suna la’akari da matsalar rashin inganci da kuma batun tsaro.
Ko da yake rahotanni sun ce an samu ɗan sassauci a rikicin, wanda ya sa farashin danyen mai ya dan sauka, har yanzu farashin fetur a Najeriya bai sauka yadda ake tsammani ba.
Masu lura da al’amura na ganin cewa wannan hali na nuna yadda rikice-rikicen duniya ke iya shafar rayuwar yau da kullum ta al’umma, ko da kuwa suna nesa da inda matsalar ta samo asali.
