News
An Samu Bullar Cutar Covid-19 A Najeriya Shekaru Bayan Duniya Ta Yi Fama Da Ita
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Cross River ta fara nema da bin sahun mutanen da suka yi mu’amala da wani dan kasar China da aka kwantar a asibiti bayan samun sa dauke da cutar Covid-19.
Kwamishinan Lafiya na jihar da ke gabar teku, Henry Ayuk, ya fadi dawowar cutar mai kisa ta SARS a babban birnin Calabar yayin zantawa sa manema labarai.
Dakarun Sojin Sama Sun Hallaka Tarin ‘Yan-Ta’adda A Dajin Sambisa
Ayuk ya ce wannan ne karo na farko da Cross River ta samu bullar cutar tun 2022 inda ya yi alkawarin za su hana cutar yaduwa.
Ya kuma ce mutumin ya zo Nijeriya a ranar 17 ga Maris din 2026, kuma ana kyautata zaton ya kamu da cutar a cikin Nijeriya bayan haura kwanaki 14 na sauraron bullar cutar inda alamunta suka bayyana a ranar 10 ga Afrilu.
Kwamishinan ya bukaci ‘yan Cross River da su kula sosai amma suna da ‘yancin ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, saboda jihar na da ikon dakilewa, yaka da hana cutar yaduwa.
Ya yi karin haske da cewa ma’aikatar a karkashin jagorancinsa ta baza ma’aikata a tsakanin al’ummar Karamar Hukumar Akampa, inda marar lafiyan yake rayuwa da aiki.
