Connect with us

News

Gwamantin Tarraya Ta Fitar Da Litar Man Jirgi Fiye Da Biliyan 1 Zuwa Turai Cikin Kwanaki 50

Published

on

1776384089487

Dai-dai lokacin da ake fuskantar ƙarancin man jirgi a Najeriya, har ma kamfanonin jiragen sama su ka yi barazanar dakatar da ayyukansu, ko kuma ruɓanya kuɗaɗen tikiti, ƙasar ta yammacin Afrika ta fitar da lita fiye da biliyan 1 na man jirgin zuwa Turai.

Wannan dai ya samo asali ne sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya da ya jefa kasuwar makamashi cikin tsaka mai wuya, har ya tilastawa ƙasashen yammacin duniya fara komawa dogara da ƙasashe irin su Najeriya don samun mai.

Advertisement

Uwa Da Danta Sun Rasu A Hatsarin Mota Yayin Shirye-Shiryen Tafiya Aikin Hajji A Kano

Wasu bayanai sun ce Najeriya wadda matatar Dangote mafi girma a Afrika ke jagorantar fannnin makamashinta, haɗin gwiwa da kamfanin mai na ƙasar NNPC sun fitar da lita biliyan 1 da miliyan 100 na man jirgi zuwa Turai cikin watanni 2 kacal,

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ce a watan Maris kaɗai Najeriya ta fitar da tan dubu 456,000, yayin da a watan Afrilun da muke ciki aka fitar da tan dubu 420,000.

Duk da cewa wannan ba ƙaramin ci gaba bane ga Najeriya musamman matatar Dangote, amma masana na ganin ƙasar ta gaza wajen wadata cikin gida da mai, maimakon haka ta mayar da hankali wajen kyautata alaƙarta da ƙasashen waje.

Advertisement

Tun watan Maris ɗin da ya gabata harkokin makamashi suka gurgunce a duniya sakamakon yaƙin Amurka da Iran, musamman ga ƙasashen Turai da suka dogara da kusan kashi 30 na man jirginsu da ake shigar musu da shi.

 

Advertisement

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending