Connect with us

News

Uwa Da Danta Sun Rasu A Hatsarin Mota Yayin Shirye-Shiryen Tafiya Aikin Hajji A Kano

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wasu maniyyata aikin Hajjin bana su biyu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Rimin Gado zuwa Kano.

‎Waɗanda suka rasu su ne Alkasim Ibrahim Walawa mai shekara 48 da mahaifiyarsa Hadiza Garba mai shekara 73.

Advertisement

JAMB Ta Fitar Da Sakamakon jarabawar UTME Na Ranar Litinin

‎Rahotanni sun ce suna kan hanyarsu ta shirye-shiryen tafiya aikin Hajji a Saudiyya lokacin da hatsarin ya rutsa da su.

Advertisement

‎A sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Sulaiman A. Dederi, ya fitar, ya bayyana cewa marigayin da mahaifiyarsa ’yan asalin ƙauyen Walawa ne a Karamar Hukumar Kabo ta Jihar Kano.

‎Alƙasim ya bar mata biyu da ’ya’ya bakwai, yayin da mahaifiyarsa ta bar ’ya’ya biyar.

Advertisement

‎Hukumar ta bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki, inda ta ce sun rasu ne a lokacin da suke shirin tafiya ibada mai tsarki.

‎Hukumar ta yi addu’ar Allah Ya gafarta musu, Ya kuma sanya su cikin Aljannatul Firdaus, tare da jajanta wa iyalan da abin ya shafa, tana mai kira gare su da su yi haƙuri da juriya a wannan lokaci mai wahala.

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending