News
Fashewar Tankar Mai Ta Hallaka Mutane 12, Ta Jikkata 38
Aƙalla mutane 12 ne suka mutu yayin da wasu kusan 38 suka jikkata sakamakon wata gobara da ta tashi bayan fashewar tankar mai a jihar Cross River da ke kudancin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba a ƙauyen Ndem, cikin ƙaramar hukumar Ogoja, a lokacin da ake aikin sauya mai daga wata tanka zuwa wata. Rahotanni sun ce tankar ta kife ta fada cikin wani kogi da ke kusa, kafin daga bisani ta kama da wuta, lamarin da ya haddasa gobara mai tsanani.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa gobarar ta bazu cikin sauri, inda ta rutsa da mutane da dama da ke wurin. Wasu daga cikin waɗanda suka rasu sun ƙone ƙurmus, lamarin da ya sa ba a iya gane su.
Wani ganau, Anthony Ekeni, ya ce ya kirga kusan mutane 38 da abin ya shafa, ciki har da gawarwaki 12 da aka tabbatar sun mutu a wurin.
Daga cikin waɗanda ake zargin sun rasu akwai shugaban ƙungiyar direbobin manyan motoci ta Ogoja da kuma wani jami’in ɗan sanda mai mukamin mataimakin sufeto (ASP), duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da sunayensu a hukumance ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda kakakinta, ASP Sunday Eitokpah, ya ce an kwashe gawarwakin tare da miƙa su ga iyalai domin gudanar da jana’iza, ciki har da al’ummar Hausawa Musulmi da abin ya shafa.
Ya kuma ƙara da cewa jami’an tsaro sun killace yankin domin hana ƙarin asarar rayuka, yayin da aka kai waɗanda suka jikkata asibitin gwamnati na Ogoja domin samun kulawa.
A cewar ‘yan sanda, an fara bincike domin gano musabbabin fashewar tankar, musamman dangane da yadda aikin sauya man ya janyo wannan gobara mai muni.
