Connect with us

News

Rikicin KCSF: An Bukaci Hadin Kan Ƙungiyoyi Domin Kare Manufofin “Kano First”

Published

on

IMG 20260518 WA0000

Daga Mohammed Bello

 

Advertisement

Ana ci gaba da nuna damuwa kan rikicin shugabanci da ya kunno kai a cikin Dandalin Kungiyoyin Fararen Hula na Kano (KCSF), yayin da masu ruwa da tsaki ke gargadin cewa rikicin na iya kawo cikas ga manufar “Kano First” idan ba a magance shi cikin adalci da gaskiya ba.

Wani masani kan bincike da tsara manufofi, Mohammed Bello, ya ce rikicin da ke cikin KCSF bai kamata a dauke shi a matsayin sabanin ra’ayi na cikin gida kawai ba, illa a kallesa a matsayin gwajin yadda kungiyar za ta iya kare martabarta da tsarin gudanarwarta.

Advertisement

Babu sojan ƙasar waje da ya shiga samamen kashe kwamandan IS —DHQ

Bello, wanda ke aiki da cibiyar African Centre for Innovative Research and Development (AFRI-CIRD), ya bayyana cewa dorewar kowace kungiyar fararen hula na rataye ne da yadda take tafiyar da harkokinta bisa gaskiya, rikon amana da kuma bayyana abubuwa a fili.

Advertisement

 

A cewarsa, duk lokacin da aka samu rauni a wadannan ginshikai, kungiyar kan rasa karfin da take da shi na neman gwamnati ko shugabanni su yi aiki da adalci da gaskiya.

Advertisement

 

“Kungiyoyin fararen hula masu karfi a duniya suna aiki ne bisa tsarin da ke tabbatar da gaskiya da bin doka. Dole ne shugabanni su kasance masu biyayya ga ka’idojin kungiyar da kuma manufofin da aka kafa ta a kai,” in ji shi.

Advertisement

 

Ya kuma nuna damuwa kan yiwuwar shigar siyasa cikin harkokin kungiyar, yana mai cewa hakan na iya lalata amincewar jama’a ga KCSF.

Advertisement

 

A cewarsa, wajibi ne kungiyar ta kasance mai zaman kanta ba tare da karkata ga wata kungiyar siyasa ko wani bangare ba.

Advertisement

 

“Idan aka fara kallon kungiyar fararen hula a matsayin mai goyon bayan wasu tsiraru ko masu ruwa da tsaki na siyasa, to za ta rasa matsayin da ake ganin tana da shi na kare muradun jama’a,” ya ce.

Advertisement

 

Mohammed Bello ya kuma bukaci duk wani yunkurin sulhu da ake yi ya kasance a bude kuma a karkashin tsarin da dukkan bangarori suka amince da shi.

Advertisement

 

Ya ce yin sulhu a boye tsakanin wasu mutane kalilan ba zai samar da cikakkiyar mafita ba, sai dai ya kara haifar da zargi da rashin yarda.

Advertisement

 

Har ila yau, ya bayyana cewa zuwa kotu bai kamata ya zama zabin farko wajen warware matsalar ba, domin irin hakan kan kara dagula rikici da raba kan mambobi.

Advertisement

 

Maimakon haka, ya ba da shawarar amfani da hanyoyin sasanci da sulhu domin dawo da hadin kai tare da kare makomar kungiyar.

Advertisement

 

“Lokaci ya yi da za a fifita maslahar kungiyar da al’umma sama da neman iko. KCSF amana ce ta jama’a, ba mallakar wasu mutane ko kungiya ba,” in ji Bello.

Advertisement

 

Ya kara da cewa idan har ana son cimma manufar “Kano First”, dole ne kungiyar ta rungumi gaskiya, adalci da kuma mutunta juna a dukkan matakan gudanarwarta.

Advertisement

 

Mohammed Bello

Advertisement

Development Research and Policy Specialist

African Centre for Innovative Research and Development (AFRI-CIRD)”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending