Connect with us

News

Babu sojan ƙasar waje da ya shiga samamen kashe kwamandan IS —DHQ

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Daraktan watsa labarai na Shelkwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Michael Onoja ya cebabu wani sojan ƙasar waje da ya taimaka wa dakarun ƙasar wajen halaka kwamandan IS, Abu Bilal Al-Minuki.

Onoja ya bayyana haka ne a hirar da ya yi da wata tashar talabijin a ƙasar, inda ya yi cikakken bayanin yadda aka aiwatar da samamen da ya kashe ƙasurgumin ɗan ta’addan.

Advertisement

Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Kano: Matashi Ya Mutu, An Kona Ofishin Ƙaramar Hukuma A Gwarzo

Ya ce abin da Amurka ta taimaka da shi gabanin wannan samame shine bayanan sirri, wanda suka yi amfani da shi wajen ƙaddamar da aikin nasu.

Advertisement

Ya ƙara da cewa aikin samamen ya bayyana irin ƙwarewa da juriya da kuma ƙarsashin da mayaƙan da suka gudanar da aikin ke da shi.

Janar ɗin ya ce rahotannin kisan Al-Manuki da sojojin Najeriya suka bayar tun da farko a shekarar 2024 kuskure ne da ya samu saboda gaza banbanta wanda aka kashe a lokacin da aininhin kwamandan, inda ya jaddada cewa yanzu dai mutumin da aka kashe shine Abu Bilal Al-Minuki, wanda yake amfani da inkiya da dama.

Advertisement

Onoja ya ce an shafe watanni da dama ana tattara bayanan da suka nuna wa dakarun Najwewriya ainihin inda ƴan ta’addan suke, yana mai cewa an ƙaddamar da harin ne bayan da kwamandojin ssoji suka tabbatar da sahihancin bayanan.

Ya ce sojin Najeriya su na cigaba da bibiyar sauran kwamandojin ƴan ta’adda har sai sun ga bayansu, inda ya kama sunan Bello Turji, yana mai cewa ba zai iya ɓuya har abada ba.

Advertisement

 

 

Advertisement

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending